TSARIN KAMA_KAMA KO NA KAMA_KARYA (Makarantu masu zaman kansu a Kano) Sanadiyyar ta6ar6arewar ilimi a makarantun kasar nan mussaman na gwamnati shi yasanya wasu daga cikin iyaye Sanya yayansu amakarantu masu zaman kansu duka dai bisa yin kuri na kama kama da gwamnati don ganin anhaifawa kasar nan nagartattun shuwagabannin gobe. Bayan da gwamnati ta bayar da wannan damar ga masu hali da su nemi abasu damar bude makarantu masu zaman kannasu a farko sai tayi wasa rai rai da shaanin makarantu, makarantun suka cigaba da cin karen babu babbaka, mussaman ta wajen cazar kudin makaranta da biyan kudin jarrabawa ta su WAEC,ko NECO,ko kuma JAMB . wadanda ka iya cewa neman kudine zalla dama masu wannan makarantu su ka fito nema don haka mutane suke ta cuku cuku da daddagewa don ganin sun yayansu makarantun lilo, To amma na tabbata wasu sun sani bawai biyan kudin ne matsala ba, face illar da ake yi ma yara ko da sanin iyayen ko ma dai ba da saninsu ba. iddan kana so ka tabbatar da abinda zan fada kakai ziyara irin wadannan makarantu ka kalli yadda yarannan ke yin shiga ta nuna tsiraici musamman mata sannan ka duba yadda su ke dan gantaka da malamansu waton su uncle, har ma ana kallon wai idan sun shiga makarantunnan wai babu haramci tsakaninsu da malaman. haka dai ake gurgurawa tsakaninsu uncle da aunty wadanda idan kana maganar Karatu sam basu kai wadancan na makarantun yashi ba sam ko kama kafarsu ma basu yi ba dalili kuwa shine dadewa a kan aiki, da ma kuma wajen daukar malami a wadancan makarantun lilon akan dauki yarane wadanda suke a makarantu kwaleji tayadda kudin da za ake basu bai taka kara ya balla ba saboda masu makarantun basu son fidda kudi su biya kwararran malami, A gaskiya dai idan kana magana akan abubuwa guda biyu kamar haka 1.Ingantacen ilimi 2.Tarbiyya yara to a Gaskiya sai muce ancuce ka don wadannan makarantun na wucin gadi sam mafi akasarinsu ba su iya baiwa yayanka wadancan abubuwa guda biyu. Dama inkana maganar hijjabi wadannan makarantu ba bu shi sam a lissafinsu,su indai zaka biya kudin makaranta to basu da matsala da kai. Game da ingantace ilimi kuwa abubuwa uku zasu tabbatar maka da cewa ba ma a gabansu ya ke ba 1.Su uncle dama ba turanci aka iya ba sai yarennan da dakaje kasuwar sabon. gari. zaka iya waton Broken English 2.Idan ka akwai ilimi da in antashi yin jarrabawa ba za a dinga baiwa yarannan satar amsa ba har su ci jarrabawa, amma kowa ya sanni Sanadiyyar makarantun lilo satar jarrabawa ta zama ruwan dare a kasar nan. 3.Za kaji yara akwai kokarin nuna su fa suna jin me kake fada da turanci amma da anje makarantun gaba da sakandare za ka tarrar sune akan gaba wajen satar amsa,sune akan gaba wajen kora daga makaranta Sanadiyyar rashin kokari a jarrabawa, sune akan gaba a wajen dandalin bata lokaci da yin soyayya. 4.Kuma da ace za ka dinga bi biyarsu a wajen karatu za ka tabbatar da cewa yawon nuna kwaliya kawai suke fita makaranta suje suyi ba karatu ba. Duk da cewa ba taruwa akayi aka zama daya ba don haka akwai wadanda suke da dan dama dama, amma duk da haka ya kamata gwamnati da alumma su dinga bibiyar wadannan makarantu don su tabbatar ba a lalata musu tarbiyar yara ba mata ba kawai har ma ta maza, kuma alummar da suke kewaye irin wadannan makarantu yakamata su dinga saya idanu akansu. kuma ita kanta gwamnati da za ta kara kula da makarantun na yashi da ai sunfi wadannan makarantun lilon da su uncle su ke tsaletsalensu. mu tuna da kanmu za muyi gyara ba wani ne zai zo yayi mana shi ba. Daga Tahir Mahmood Saleh
TSARIN KAMA_KAMA KO NA KAMA_KARYA (Makarantu
ReplyDeletemasu zaman kansu a Kano)
Sanadiyyar ta6ar6arewar ilimi a makarantun kasar nan
mussaman na gwamnati shi yasanya wasu daga cikin
iyaye Sanya yayansu amakarantu masu zaman kansu
duka dai bisa yin kuri na kama kama da gwamnati don
ganin anhaifawa kasar nan nagartattun shuwagabannin
gobe.
Bayan da gwamnati ta bayar da wannan damar ga
masu hali da su nemi abasu damar bude makarantu
masu zaman kannasu a farko sai tayi wasa rai rai da
shaanin makarantu, makarantun suka cigaba da cin
karen babu babbaka, mussaman ta wajen cazar kudin
makaranta da biyan kudin jarrabawa ta su WAEC,ko
NECO,ko kuma JAMB . wadanda ka iya cewa neman
kudine zalla dama masu wannan makarantu su ka fito
nema don haka mutane suke ta cuku cuku da
daddagewa don ganin sun yayansu makarantun lilo,
To amma na tabbata wasu sun sani bawai biyan kudin
ne matsala ba, face illar da ake yi ma yara ko da sanin
iyayen ko ma dai ba da saninsu ba. iddan kana so ka
tabbatar da abinda zan fada kakai ziyara irin wadannan
makarantu ka kalli yadda yarannan ke yin shiga ta nuna
tsiraici musamman mata sannan ka duba yadda su ke
dan gantaka da malamansu waton su uncle, har ma
ana kallon wai idan sun shiga makarantunnan wai babu
haramci tsakaninsu da malaman. haka dai ake
gurgurawa tsakaninsu uncle da aunty wadanda idan
kana maganar Karatu sam basu kai wadancan na
makarantun yashi ba sam ko kama kafarsu ma basu yi
ba dalili kuwa shine dadewa a kan aiki, da ma kuma
wajen daukar malami a wadancan makarantun lilon
akan dauki yarane wadanda suke a makarantu kwaleji
tayadda kudin da za ake basu bai taka kara ya balla ba
saboda masu makarantun basu son fidda kudi su biya
kwararran malami,
A gaskiya dai idan kana magana akan abubuwa guda
biyu kamar haka
1.Ingantacen ilimi
2.Tarbiyya yara
to a Gaskiya sai muce ancuce ka don wadannan
makarantun na wucin gadi sam mafi akasarinsu ba su
iya baiwa yayanka wadancan abubuwa guda biyu.
Dama inkana maganar hijjabi wadannan makarantu ba
bu shi sam a lissafinsu,su indai zaka biya kudin
makaranta to basu da matsala da kai.
Game da ingantace ilimi kuwa abubuwa uku zasu
tabbatar maka da cewa ba ma a gabansu ya ke ba
1.Su uncle dama ba turanci aka iya ba sai yarennan da
dakaje kasuwar sabon. gari. zaka iya waton Broken
English
2.Idan ka akwai ilimi da in antashi yin jarrabawa ba za
a dinga baiwa yarannan satar amsa ba har su ci
jarrabawa, amma kowa ya sanni Sanadiyyar
makarantun lilo satar jarrabawa ta zama ruwan dare a
kasar nan.
3.Za kaji yara akwai kokarin nuna su fa suna jin me
kake fada da turanci amma da anje makarantun gaba
da sakandare za ka tarrar sune akan gaba wajen satar
amsa,sune akan gaba wajen kora daga makaranta
Sanadiyyar rashin kokari a jarrabawa, sune akan gaba a
wajen dandalin bata lokaci da yin soyayya.
4.Kuma da ace za ka dinga bi biyarsu a wajen karatu
za ka tabbatar da cewa yawon nuna kwaliya kawai suke
fita makaranta suje suyi ba karatu ba.
Duk da cewa ba taruwa akayi aka zama daya ba don
haka akwai wadanda suke da dan dama dama, amma
duk da haka ya kamata gwamnati da alumma su dinga
bibiyar wadannan makarantu don su tabbatar ba a
lalata musu tarbiyar yara ba mata ba kawai har ma ta
maza, kuma alummar da suke kewaye irin wadannan
makarantu yakamata su dinga saya idanu akansu.
kuma ita kanta gwamnati da za ta kara kula da
makarantun na yashi da ai sunfi wadannan makarantun
lilon da su uncle su ke tsaletsalensu.
mu tuna da kanmu za muyi gyara ba wani ne zai zo
yayi mana shi ba.
Daga Tahir Mahmood Saleh